Bayan fitowa daga gidan yarin Joshua Dariye na shirin tsayawa takarar sanata

0

Matukar ba a samu sauyi daga baya ba to kuwa tsohon gwamnan jihar Filato, Joshua Dariye zai ayyana aniyarsa ta tsayawa takarar majalisar dattawa mai wakiltar mazabar Filato ta Tsakiya a karkashin jam’iyyar LP.

Dariye da kuma tsohon gwamnan jihar Taraba, Joly Nyame na daga cikin waɗanda aka saka daga gidan yarin Kuje watanni uku bayan da majalisar kolin ƙasa da shugaban kasa, Buhari yake jagoranta tayi musu afuwa.

Bayanan da jaridar Daily Trust ta tattara sun nuna cewa jam’iyyar LP reshen jihar Filato ta kammala shirye-shiryen tarbar tsohon gwamnan daga Abuja domin ta bashi fom din takara.

Wani jami’i a jam’iyar ta Labour Party da ya bukaci a boye sunansa ya fadawa jaridar cewa tabbas suna shirye-shiryen zuwan Dariye domin yazo ya ayyana takararsa kuma suna da yakinin zai bada mamaki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here