Kabiru Agbabiaka Osolo na Isolo dake jihar Lagos ya rasu.
Basaraken na jihar Lagos ya rasu ne da safiyar ranar Laraba.
A wata sanarwa Olasoju Adebayo shugaban ƙaramar hukumar mulki ta Isolo ya ce an gudanar da jana’izar marigayin a ranar Laraba da ƙarfe 4 na yamma.
“Yana da shekaru 64 za ayi jana’izarsa yau ƙarfe 4 a fadarsa dake layin Akinbaye Isolo kamar yadda addinin musulunci ya tanada,” a cewar sanarwar.
Shugaban ƙaramar hukumar bai bayyana dalilin mutuwar marigayin ba sai dai wasu majiyoyi sun bayyana marigayin ya halarci Sallar Idin ƙaramar sallah da aka yi a ranar.