Barazanar durkushewar harshe: Abin da ya ci Doma ba zai bar Awai ba, daga Hamza Darazo

A fannin ilimin walwalar harshe ko kuma nazarin harshe da al’umma wato ‘sociolinguistics’ akwai abinda ake ce wa ‘Language endangerment’. Shi wannan wani yanayi na hadari ko barazanar durkushewa ( a wani lokaci har mutuwa) ne da harshe (language) kan tsinci kansa a ciki sakamakon ya rasa masu magana da shi, sai ya kasance ya wofinta, ya zamo matacce. Akwai dalilai masu yawa da suke haddasa durkushewar harshe ko mutuwarsa gaba-daya. Zai iya kasancewa dalilin wasu masifu ko bala’o’i (natural disasters) da suka samu al’umma. Ko dalilan yaki da kuma mamayar al’umma da makamantansu.

Saboda dalilai mabambanta, wasu mutane kan ajiye harshensu na uwa su rungumi wani harshen da ya fi nasu tasiri kuma yake da fifiko a cikin al’ummar da suke rayuwa. Dalilin haka sai ya zamo hatta iyaye, wadanda su ne tushe kuma matakin farko na koyo da magana da harshen uwa ga ‘ya’yansu sukan fi amfani da wannan harshen da ya fi tasiri da fifiko wajen sadarwarsu da ‘ya’yan nasu, sabanin harshensu na asali. Da zarar an samu haka, ba shakka sai hanya ko mahadar da ke gadar da harshen uwa ga ‘ya’ya ta katse. A karshe sai ya zamo mutanen da ke amfani da harshen uwarsu ‘yan ƙalilan ne ainun. Daga karshe sai harshen ya shiga wani yanayi mai kama da rashin lafiya, ya fara fuskantar barazanar durkushewa har wata rana ya bata bat, a daina amfani da shi, a neme shi ko kuma masu magana da shi a rasa.

Wani bincike da aka yi shekaru biyu da suka gabata ya nuna harsuna 42 ne suke cikin irin wannan yanayin na yiwuwar mutuwa a kowane lokaci a kasar Indiya. A shekarar 2014, binciken kwararru ya tabbatar da wasu harsuna 25 na duniya da suke cikin tsananin gargarar mutuwa, wasun su ma har sun mutu gaba-daya.

A wani bincike da UNESCO ta fitar, ta bayyana cewa zuwa yanzu mutum daya tal ne aka sani wanda ya iya magana da harshen ‘Apiaka’ da ke ‘Mato Grosso’ a kasar Brazil. Al’ummar sun rungumi harshen ‘Potuguese’ sabanin nasu.

A wasu lokutan kuma akan samu yanayin da za a tarar kalmomin harshe da dama sun bace bat; kamar ba a yi su ba, hakan yana faruwa a sakamakon fifita amfani da kalmomin harshen da ake ganin ya fi tasiri ko fifiko, ba wai don harshen uwa da ake amfani da shi ba shi da wadannan kalmomin ba, sai don kawai ana ganin wancan harshen ya fi fifiko. A dalilin haka sai ka ga mutum yana magana da harshensa na uwa, a lokaci guda kuma yana sakada kalmomin harshen da ya tasirantu da shi. Ko kuma a wasu lokutan ma ya koma amfani da harshen gaba daya. Wannan al’amari ba karamin tauye harshen uwa yake ba. Sannan ya canza masa daraja da matsayi daga hakikar yadda yake a da, da kuma taimakawa wajen mutuwar harshen, ta fuskacin batar da kalmomi da daman gaske. Sai a wayi gari kamar da ma can babu wadannan kalmomin a harshen.

Duba da yadda matasanmu suka riki wasu harsunan duniya, musamman harshen Turanci, suka fifita shi a kan harshenmu na uwa a mu’amalolinsu na rayuwa musamman a birane, in ba a yi hankali ba akwai barazanar yiwuwar tsirar harsashin tauyewar harshenmu Hausa nan gaba.

Bai boyu ga kowa ba, yadda amfani da Turanci ya fi zama abin burgewa da gwarzantaka a tsakanin al’ummarmu musamman matasa . A yau wanda bai iya magana da Turanci ba, to bai san komai ba, ya rasa kima balle a darajta shi a tsakanin mafi yawan mutane. Hausa kuwa, duk iyawarka ba za ka wani burge ba balle ka samu yabo. In ko har ka ja hankalin mutane da harshen Hausa har suka gan ka a matsayin mutum mai daraja mai ilimi, to lallai ka gwanance ka zama fasihin iya magana ta amfani da dabarun sarrafa harshe da zantuttukan hikima ne ko wasu dalilai da aka yarda da su.

Duk da cewa ba lallai kowa ya yarda ba, amma wannan hanyar da muke a kai a yau ta sa na kara tabbatar da cewa har yau ba mu samu ‘yancin da muke ikirarin an ba mu ba shekaru 59 baya, a kaddara ma mun samu ‘yancin mulkin kai, amma fa akwai sauran rina a kaba, saboda har yau din nan, manyan harsunan da muke da su a wannan kasa tamu, babu daya daga cikinsu da ya ‘yantu. Babu daya daga cikin harsunan wanda ake amfani da shi wajen koyarwa a makarantun Gwamnati ko a ma’aikatu da ofisoshi. Haka kuma ba su samu tagomashin a-zo-a-gani ba a manyan jaridu na kasa, ballantana su yi zarra.

Idan abin a yi dubi da ire-iren wadannan wuraren ne, za ma a iya cewa harsunan mutanen kasar nan na uwa duk sun mutu. Idan kuma ba a yi taka-tsantsan ba, abin da ya ci Doma ba zai bar Awai ba.

Ba shakka wannan lamarin yana taka muguwar rawa wajen kawo nakasu a fannonin iliminmu da fasaharmu da fikirarmu da kuma wayewarmu.

Allah ya ‘yantar da mu.

Hamza Darazo ne ya rubuto wannan makala daga Bauchi. Za a iya samunsa ta 0706 329 9695.

More from this stream

Recomended