Ba za mu iya aiwatar da buƙatun Nyesom Wike ba – Jam’iyyar PDP

0

Da alama har yanzu tana kasa tana dabo a babbar jami’iyyar hamayya ta Najeriya, PDP, game da rikicin da ke ci gaba da gwara kan ƴaƴan jam’iyyar bayan da gwamnan Rivers Nyesom Wike ya tsaya kai da fata kan ƙudurinsa na ganin an sauke shugaban jam’iyyar Iyorchia Ayu, duk kuwa da ƙuri’ar amincewa da shugabancin jam’iyyar da aka kaɗa a ranar Alhamis ɗin da ta gabata.

Jam’iyyar dai ta shiga cikin ruɗani ne tun bayan zaɓen fitar da gwani na ɗan takarar shugaban ƙasa da ta gudanar, inda Atiku Abubakar ya yi nasara a kan sauran masu neman jam’iyyar ta tsayar da su takara.

Amma a lokacin taron shugabanninta da ya gudana a baya-bayan nan ne, mahalarta suka amince Iyorchia Ayu ya ci gaba da tafiyar da lamuran jam’iyyar duk da kafewar da ɓangaren gwamna Wike ke yi na a sauke shi daga muƙamin.

Sanata Umar Ibrahim Tsauri, mamba a kwamitin amintattu na jam’iyyar ta PDP, ya shaida wa BBC cewa nan da mako guda za su iya sasanta rikicin da suke fama da shi na cikin gida saboda “jam’iyyar siyasa ce mai mutane masu mutunci da ƙima da daraja da tunani da hankali”.

Da yake magana game da Nyesom Wike, Sanata Tsauri ya ce gwamnan na Rivers ba ƙashin yadawa bane saboda yana da ƙwarewa kuma “abin da ake so yanzu shi ne a yi ƙoƙari a dawo da shi, wancan tunanin na shi ya rage ya dawo a yi jam’iyyar PDP.”

Ya ce buƙatar Wike ta ganin an sauke Ayu abu ne ba mai yiwuwa ba saboda ɗaukar matakin a irin wannan lokacin sam ba zai ciyar da jam’iyyarsu gaba ba musamman ganin yadda ake tunkarar zaɓen 2023.

“Komai yana da lokacinsa, idan ka ce za ka cire shugaban PDP yanzu, misali, kuma ka mayar da shi kudu, tor sai an yi babban taro domin tsarin mulkin PDP abin da ya ce shi ne idan shugaba ya sauka, tor mataimakinsa na sashen da ya fito, shi zai ɗauka.” kamar yadda ya faɗa.

Buƙatun da Wike ya gabatar

Sanata Tsauri ya ce akwai buƙatu shida da Nyesom Wike ya gabatar amma ya shaida wa BBC guda huɗu.

  • Neman a sauke Iyorchia Ayu daga Shugabancin PDP – “ba za a ce ba zai yiwuwa amma yinsa ba dai-dai bane saboda lokaci”.
  • Atiku ya sa hannu cewa zai yi zangon mulki guda wanda a cewar Sanata Tsauri “babu wanda zai rubuta takarda ya ce zangon mulki daya zai yi.”
  • Buƙatar a janye gwamna Ifeanyi Okowa a matsayin wanda zai marawa Atiku Abubakar a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
  • Sannan neman idan an tashi rabon muƙamai a basu (ɓangaren gwamna Wike) na shugaban ƙasa.

[