Mutum biyu daga cikin masu takarar gwamna a jihar Buachi da ke arewacin Najeriya karkashin jam’iyyar APC sun ce ba za su ci gaba da kasancewa a zaben fitar da gwani ba, har sai uwar jam’iyyar ta kasa ta dakatar da gwamnan jihar Muhammad Abdullahi Abubakar da kuma shugabannin jam’iyyar a matakin jiha daga cikin jam’iyyar.
Dr Ibrahim Yakubu Lame da Dr Muhammad Ali Pate sun kuma ce dole sai an hana gwamnan yin takarar.
Mutane biyun dai na daga cikin mutane uku da ke fafatawa da gwamnan a zaben fitar da gwani na jam’iyyar wanda ya ci tura duk da kwashe yini biyu ana kokarin gudanar da shi.
Sun bayyana bukatar tasu ce a sakatariyar jam’iyyar APC a ranar Litinin da daddare.
Sai dai BBC ta yi kokarin jin ta bakin jam’iyyar amma hakan ya ci tura.
Amma kwamishinan yada labarai na jihar Buachin ya ce batun nasu zancen banza ne.