Ba maganar sulhu tsakanina da Ganduje – Kwankwaso

Tsohon gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya musanta wasu raɗe-raɗi da ke yawo da ke bayyana cewa yana tattaunawa da gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje don yin sulhu.

Yayin wata hira da Channels TV da yammacin ranar Lahadi. Kwankwaso ya ce ya ji daɗin ziyarar ta’aziyyar da Ganduje ya kai masa kwanakin baya, amma bayan wannan ziyara ta gaisuwa babu wata magana da ake yi a bayan fage dangane da yin sasantawa.

Ya bayyana yadda alaƙarsa ta kasance da Gandujen a baya tun lokacin da ya yi mata mataimakin gwamnan Kano a zaɓen 1999, da kuma yadda suka ci gaba da aiki tare har zuwa 2015 lokacin da suka raba garin bayan ya zama gwamna.

An tambaye shi cewa to shin yanzu idan ka samu wata dama za ka sake bayar da sunan Ganduje kamar yadda ka yi a baya ?.

Sai ya kada baki ya ce ”A yanzu dai ka san ba a jam’iyya ɗaya muke ba, don haka ina ga babu ma buƙatar yin wannan tambaya, don haka ko da dama ta samu akwai mutanen da suka cancanta cikin waɗanda nake tare da su”.

Alaƙa tsakanin shugabannin biyu ta daɗe da lalacewa tun bayan da Kwankwaso ya miƙa wa Ganduje ragamar mulkin Kano a 2015 bayan sun shafe shekara takwas a matsayin gwamna da mataimaki. har ta kai ga yanzu Kwankwaso ya koma jam’iyyar adawa ta PDP.

Sai dai Gwamna Ganduje na ci gaba da fuskantar rikicin cikin gida a jam’iyyarsu ta APC tsakaninsa tawagar tsohon gwamna kuma sanata a yanzu, Malam Ibrahim Shekarau.

Rikicin siyasar Kano dai na ci gaba da kankama musamman a jam’iyyar APC mai mulki, inda tsagin tsohon gwamnan jihar Malam Ibrahim Shekarau ke rikici da ɓangaren Ganduje kan shugabancin jam’iyya.

Haka ma a PDP har yanzu tana ƙasa tana dabo tsakanin ɓangaren Kwankwaso da na tsohon ministan harkokin wajen Najeriya Ambasada Aminu Wali, wanda shima ɓangarensa ke adawa da jagorancin Kwankwaso.

More News

Bayan fitowa daga gidan yarin Joshua Dariye na shirin tsayawa takarar sanata

Matukar ba a samu sauyi daga baya ba to kuwa tsohon gwamnan jihar Filato, Joshua Dariye zai ayyana aniyarsa ta tsayawa takarar majalisar dattawa...

Duk wanda ya ce Najeriya kalau ta ke to a binciki kansa-Obasanjo

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya ce har yanzu Najeriya ba ta kai matakin da yakamata ace ta kai ba a yanzu. A cewar...

Yan bindiga sun sako karin mutane 7 daga cikin fasinjojin jirgin kasar Abuja zuwa Kaduna

Yan bindiga da suka yi garkuwa da fasinjojin jirgin kasar da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna sun kara sako mutanen 7 daga cikin...

Farashin ɗanyen man fetur ya yi kasa a kasuwar duniya

Farashin gangar danyen mai ya fado kasa da dala $95 a ranar Talata. Faduwar tasa na zuwa ne biyo bayan saka ran da ake na...