Atiku zai yi taro da ƴan jaridu

Atiku Abubakar ɗan takarar shugaban kasa a jam’iyar PDP a zaɓen da ya wuce zai yi taron manema labarai a ranar Alhamis 5 ga watan Oktoba.

Dele Momodu wanda shi ne daraktan yaɗa labarai na kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyar PDP shi ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Dele ya bayyana cewa za a yaɗa ganawar kai tsaye ta shafukan sada zumunta na Atiku da kuma gidajen yaɗa labarai na gida da waje.

Duk da cewa ba a bayyana dalilin ganawa da ƴan jaridun ba ana ganin za ta fi mai da hankali kan batun shari’ar zaɓen shugaban ƙasa dake gaban kotun ƙoli da kuma batun takardun karatun shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.

More News

Tsoffin gwamnoni sun wawashe sama da naira tiriliyan 2 tun komawa dimokuraɗiyya

Aƙalla tsoffin gwamnoni 58 ne ake zargin sun wawure kuma sun yi almubazzarancin jimillar naira Tiriliyan 2.187 a cikin shekaru 25 tun komawa mulkin...

Ƴan sanda sun kama mutane 50 kan rikicin da ya faru a wata kasuwa a Lagos

Rundunar ƴan sandan jihar Legas ta kama mutane sama da 50 da ake zargin suna da hannu rikicin da ya faru a kasuwar Ile...

Ƴan Sanda sun kama wanda ya shirya kai harin jirgin ƙasar Abuja-Kaduna a shekarar 2022

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce jami'anta sun kama wani mutum mai suna Ibrahim Abdullahi wanda ake zargi da kitsa harin jirgin ƙasar da...

Ƴansanda sun kama wanda ya kitsa harin da aka kai wa jirgin ƙasa a Kaduna

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a ranar Alhamis, ta sanar da kame wanda ake zargin ya shirya harin da aka kai a jirgin ƙasan Abuja-Kaduna...