Asibiti sun hana iyaye gawar dansu don gaza biyan kudi | BBC Hausa

'Yan tasi da babura a asibiti

Hakkin mallakar hoto
RSUP M Djamil

Image caption

An dauki bidiyon yadda ‘yan tasi da baburan suka mamaye asibitin

‘Yan tasi da babura sun cika wani aibiti Indonesiya a wani mataki da suka ce na jin kai ne, bayan hukumomin asibitin sun ki bayar da gawar jaririn kan rashin biyan kudin asibiti.

Lamarin ya faru ne a babban asibitin birnin Padang, an kuma yada hotuna da bidiyon yadda mutanen suka shiga asibitin da kuma yadda wani ya dauko gawar jariri Alit Putr a kafadarsa.

A tsari da ka’idar addinin musulunci dai ba a jinkirta binne mamaci, sai da wani kwakkwaran dalili.

Daya daga cikin mutanen Wardiansyah ya shaida wa sashen BBC Indonesia cewa ”Mun dauki matakin ne don an rike gawar yaron saboda iyayensa ba su biya kudin asibiti ba, ba za su iya biyan rufiya miliyan 25 ba, kwatankwacin dala 1,774.”

Ya kara da cewa jami’an tsaro sun yi kokarin hana su shiga asibitin, saboda sun taho zuga guda.

Bidiyon lamarin ya bazu kamar wutar daji a shafukan sada zumunta. Kuma ya janyo zazzafar muhawara kan yadda ake wulakanta iyaye ko ‘yan uwan marasa lafiya a asibitocin, musamman wadanda suka gagara biyan kudin magani.

A baya dai akwai korafe-korafe kan jami’an wasu asibitoci, kan yadda suke garkuwa da jariran da aka haifa har sai iyaye sun biya kudaden da aka caje su.

Image caption

Gwamman masu baburan sun fi karfin jami’an tsaron

An gudanar da shirin tsarin lafiya na bai daya a baki dayan kasar karkashin mulkin Shugaba Joko Widodo, sai dai shirin ya gamu da tangarda sakamakon rashin kudin tallafi, kuma yawancin iyalai matalauta sun gagara yin rijista.

Mahaifiyar yaron, Dewi Surya, ta ce sun fara shirin yin rijistar sai dansu Alif ya fara rashin lafiya.

Da suka kai shi asibiti, likitoci suka bukaci a yi masa aiki, an yi da kwana biyu Alif ya rasu a ranar Talata.

“Asibitin sun ce sai mun biya kudin aikin, ana ta jan maganar da fafutukar yadda za a biya kudin,” in ji ta. ”Direbobin sun ji haushin abin da akai mana, don haka suka dauki gawar Alif ta karfin tuwo.”

Cikin kuka Surya a lokacin da ake yi wa dan nata sutura ta kara da cewa: ”Allah sarki Alif, ana ta ce-ce-ku-ce akan bayar da gawarsa wadda aka ajiye a mutuware.”

Daga bisani hukumomin asibitin sun bayar da hakuri, tare da alkawarin hakan ba za ta sake faruwa ga wani mara lafiya ba.

Hakkin mallakar hoto
Halbert Caniago

Image caption

Dewi Surya kenan cikin kuka jim kadan bayan an tafi binne Alif

Daraktan asibitin Yusirwan Yusuf ya ce asibitin ya yafewa iyayen Alif kudin, tare da bayyana lamarin a matsayin rashin fahimta.

”Sai bayan da iyayen yaron suka shigar da korafi ga hukumomin asibitinmu, sannan muka san abin da ya faru.” Ya kara da cewa ”Wannan asibitin na gwamnati ne, ba mu taba bukatar kudi daga marasa lafiya ba.”

Mista Yusuf ya soki abin da direbobin tasi da baburan suka yi a asibitin, ya ce abin bai dace ba sam.

”Muna da tsarin yadda ake tafiyar lamarin irin wannan, amma abin da suka yi ya sabawa dokar asibitinmu.”

Su ma wakilan ‘yan tasi da baburan sun nemi afuwar hukumomin asibitin, kan yadda suka mamaye shi da tilasta daukar gawar yaron.

Daya daga cikin wakilansu Alfiandri ya shaida wa BBC cewa ”A madadina da abokan aikina, muna neman afuwar asibitin nan kan abin da muka yi, ba mu yi hakan don wulakanta sunan asibitin ba.

“Abin da ya ba mu haushi shi ne yadda ake ta jan kafa wajen bayar da gawar Alif, don haka muka dauki mataki da kanmu.” in ji Alfiandri.

Rahoto daga Sita Dewi ta BBC Indonesia

More from this stream

Recomended