Arsenal na dab da daukar Nicolas Pepe daga Lille

Nicolas Pepe

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Pepe ya ci kwallo 23 a wasa 41 a Lille a kakar da ta gabata

Arsenal ta cimma yarjejeniya da kulob din Lille na Faransa domin sayen dan wasan gefe na Ivory Coast Nicolas Pepe kan fam miliyan 72.

Gunners za su biya kudin a hankali domin ya yi daidai da karfin aljihunsu.

Amma har yanzu ba a kammala yarjejeniya tsakanin Arsenal da wakilan Pepe ba.

Sai dai ana sa ran za a karkare komai nan da kwana daya ko biyu.

Napoli ma sun amince su biya farashin da Lille ta sanyawa dan wasan sai dai sun kasa cimma matsaya da wakilansa.

Pepe ya ci kwallo 23 a wasa 41 a Lille a kakar da ta gabata.

Arsenal sun taya dan wasan Crystal Palace da Ivory Coast Wilfried Zaha a farkon watan nan fan miliyan 40 amma Palace sun yi wa dan kwallon farashin fam miliyan 80.

More from this stream

Recomended