Arsenal da Inter Milan na zawarcin Griezmann, Salah zai zauna a Liverpool “tsawon lokaci”

0

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Fafutukar da dan wasanBarcelona Antoine Griezmann yake yi ta samun shiga a kungiyar ka iya bai wa Arsenal ko Inter Milan damar dauko dan wasan na Faransa mai shekara 29. (Express)

Arsenal tana fatan ganin David Luiz, mai shekara 33, ya iya rarrashin dan kasarsu ta Brazil Thiago Silva, mai shekara 35, ya koma kungiyar idan ya bar Paris St-Germain a bazara. (Le10 Sport, via Mail)

Kazalika Arsenal ta kara kaimi a yunkurinta na dauko dan wasan tsakiyar Atletico Madrid Thomas Partey sai dai ba za ta biya zunzurutun kudin da ya kai £45m don karbo shi ba. (Athletic, via Mirror)

Dan wasanTottenham daIvory Coast Serge Aurier, mai shekara 27, yana burge Monaco, wacce take fatan dauko shi a bazarar nan. (Sky Sports)

Dan wasanChelseadan kasar Denmark Andreas Christensen, mai shekara 24, ya ce ba shi da niyyar barin kungiyar kuma yana son sabunta kwangilarsa a Stamford Bridge. (Goal.com)

Dan wasan Arsenal da Armenia Henrikh Mkhitaryan, mai shekara 31, ya shirya tsaf don komawa Roma dindindin idan aka tsawaita zaman aron da yake yi a can. Sai dai mai yiwuwa dan wasan Netherlands Justin Kluivert, mai shekara 21, ba zai koma Arsenal ba. (Mail)

Kocin Barcelona Quique Setien yana shan karin matsin lamba kuma an ga kocin Netherlands Ronald Koeman, wanda ya ce ya ki amsa tayin komawa Nou Camp a watan Janairu, yana tarewa a sabon gida a birnin. (Mail)

Dan wasanLiverpool da Masar Mohamed Salah, mai shekara 28, ya ce yana son zama a kungiyarr “na tsawon lokaci”. (Bein Sports, via Express)

Matashin dan wasanManchester United Largie Ramazani, dan shekara 19, yana dab da komawa kungiyar kwallon kafar Almeria da ke kasar Sufaniya. Da wasan na Belgium ya yi watsi da tayin ci gaba da zama a Old Trafford. (Manchester Evening News)

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here