APC ta lashe zaben gwamnan Ekiti

Abiodun Oyebanji dan takarar jam’iyar APC a zaben gwamnan jihar Ekiti da aka gudanar ranar Asabar shi aka ayyana a matsayin Wanda ya lashe zaben.

Oyebanji wanda ya samu nasara a kananan hukumomi 15 cikin 16 dake jihar ya samu jumullar kuri’a 187057.

Tsohon gwamnan jihar,Segun Oni na jam’iyar SDP shi ne yazo na biyu da kuri’a 82211 sai kuma Bisi Kolawole na jam’iyar PDP da ya samu kuri’a 67457.

Jami’in tattara sakamakon zaben, Farfesa Kayode Oyebode shi ne ya sanar da nasarar da Oyebanji yayi da misalin karfe 3:04 na daren ranar Lahadi.

Yan takara 16 ne suka tsaya takara a zaɓen.

Ga sakamakon da kowacce jam’iya ta samu:

A: 166
AAC: 409
ADC: 5,597
ADP: 3,495
APC: 187,057
APGA: 376
APM: 290
APP: 1,980
LP: 195
NNPP: 529
NRM:347
PDP: 67,457
PRP: 856
SDP: 82,211
YPP: 618
ZLP: 282

More News

ÆŠalibai a Jami’ar Jos na zanga-zanga saboda rashin wuta da ruwa

Wasu daliban jami’ar Jos da ke jihar Filato a ranar Alhamis sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matsalar karancin ruwa da rashin...

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...