Ana zargin yan Okada da kashe ɗan sanda a Lagos

An samu tashin tarzoma akan babbar hanyar Apapa-Oshodi dake birnin Lagos bayan da aka zargi yan Okada da kashe wani ɗan sanda.

Akalla bindigogi uku mallakar yan sandan ake zargin an yi awon gaba da su a lokacin rikicin.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa lamarin ya faru a wurin dauka da ajiye fasinjoji na Cele Bus Stop hakan ya kuma ya jefa tsoro a zukatan al’ummar yankin.

Anga motocin yan sandan cikin shirin ko ta kwana a yankin a yayin da yan Okada suka yi dandazo dauke da sanduna, adduna da kuma sauran makamai.

Har ya zuwa rubuta wannan labari babu cikakken bayanin da ya fito kan dalilin da ya haddasa rikicin.

Su

More from this stream

Recomended