An yi wa Casemiro sata lokacin da ake wasan hamayya

Casemiro

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Matar Casemiro da dansa suna cikin koshin lafiya amma an debi kayayyaki

Yayin da Casemiro ke fafata wa Real Madrid wasa a wasan hamayyar birnin Madrid a filin wasa na Wanda Metropolitano, wasu sun haura gidansa sun yi sata yayin da matarsa da dansa suke ciki.

Wasan hamayyar na birnin Madrid dai ya tashi 0-0 ne, inda Atletico Madrid ba ta iya karya kwarin Real Madrid ba na wasa bakwai a La Liga ba tare da rashin nasara ba.

Matarsa da dan nasa suna cikin koshin lafiya amma an yi awon gaba da wassu kayayyaki daga gidan dan kasar Brazil din.

El Chiringuito ta ruwaito cewa Casemiro shi ne dan wasa na baya-bayan nan da aka haura gidansa a ‘yan kwanakin nan.

Real Madrid ta sha gargadin ‘yan wasanta da su daina saka hoton gidajensu a shafukan sada zumunta saboda dalilan tsaro.

More from this stream

Recomended