Fasinjoji 15 aka yi awon gaba da su inda aka tasa ƙeyarsu ya zuwa cikin daji dake tsakanin garin Donga-Maraban Baissa dake ƙaramar hukumar Donga ta jihar Taraba a ranar Litinin.
Fasinjojin da suka haɗa da mata da ƙananan yara na kan hanyarsu ta dawowa daga Zaki-Biam a jihar Benue ya zuwa garin Maihula dake ƙaramar hukumar Bali lokacin da suka Afkawa shingen masu garkuwa da mutanen.
Wasu daga cikin fasinjojin ciki har da direban motar sun samu nasarar tserewa ya zuwa cikin daji inda suka yi tafiyar kusan kilomita 100 a ƙafa kafin su isa garin mai hula.
Musa Tanko wani mazaunin Maihula ya faɗawa jaridar Daily Trust cewa dukkanin fasinjojin mazauna garin Maihula ne kuma suna kan hanyarsu ne ta komawa Maihula daga Zaki-Biam inda suka faɗa shingen da masu garkuwa da mutane suka saka a wani daji dake Maraban Baissa.
Ƙoƙarin da jaridar Daily Trust ta yi na jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar ya ci tura.