Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wasu mutane biyu a yankin Gumau da ke karamar hukumar Toro a jihar Bauchi.
An ce ‘yan bindigar sun yi harbin iska ne don tsorata mazauna yankin kafin su tafi da wadanda abin ya shafa a safiyar ranar Asabar.
Da yake mayar da martani kan lamarin, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Toro a majalisar wakilai, Hon Dabo Ismail Haruna, ya yi Allah wadai da sace sacen da aka yi kwanan nan.
Ya ce ‘yan bindigar sun dawo suna addabar al’umma ta hanyar yin garkuwa da su ba tare da kakkautawa ba domin neman kudin fansa bayan wani lokaci.Sai dai ya ba wa ‘yan mazaɓar tasa tabbacin shiga tsakani na ‘yan majalisu da za su kawo karshen abubuwan da ba su dace ba, ya kara da cewa yawaitar sace-sacen jama’a a mazabar tarayya ta Toro ya haifar da damuwa sosai a jihar.
Haruna ya yi kira ga gwamnan jihar Sen. Bala Mohammed da gwamnatin tarayya da su gaggauta tura karin jami’an tsaro zuwa karamar hukumar domin kamo miyagu.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Ahmed Wakili, bai amsa sakonni ba da kuma kiran da aka yi masa domin tabbatar da faruwar lamarin kafin ya rubuta wannan rahoto.
Sai dai ya ba wa ‘yan mazaɓar tasa tabbacin shiga tsakani na ‘yan majalisu da za su kawo karshen abubuwan da ba su dace ba, ya kara da cewa yawaitar sace-sacen jama’a a mazabar tarayya ta Toro ya haifar da damuwa sosai a jihar.
Haruna ya yi kira ga gwamnan jihar Sen. Bala Mohammed da gwamnatin tarayya da su gaggauta tura karin jami’an tsaro zuwa karamar hukumar domin kamo miyagu.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Ahmed Wakili, bai amsa sakonni ba da kuma kiran da aka yi masa domin tabbatar da faruwar lamarin kafin rubuta wannan rahoto.