An samu tashin hankali a yankin Kagarko da ke kudancin Kaduna, inda rahotanni suka ce wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki fadar Sarkin Kagarko, inda suka yi garkuwa da ‘ya’yansa tara da wata matarsa.
Rahotanni da dama daga jihar sun nuna cewa ‘yan bindigar sun kai farmaki yankin ne da misalin karfe 11:15 na dare, sun kuma tafi da jikokin sarkin da wasu mazauna yankin guda uku.