An tsaurara matakan tsaro a kotun da ake shari’ar zaben shugaban ƙasa

Jami’an tsaro dauke da makamai sun killace tituna zuwa kotun shari’ar zaben shugaban kasa a ranar Laraba da ke Abuja.

An gindaya shingayen binciken ababen hawa guda uku tsakanin hedkwatar ma’aikatar kudi da kofar kotun.

Ana sa ran kotun za ta yanke hukunci kan koke-koken zaben da ke kalubalantar zaben shugaba Bola Tinubu da ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party, Atiku Abubakar, da kuma Peter Obi na jam’iyyar Labour Party suka yi.

More from this stream

Recomended