An tsaurara matakan tsaro a Daura gabanin komawar Buhari gida

An tsaurara matakan tsaro a Daura mahaifar shugaban kasa, Muhammad Buhari gabanin dawowarsa gida bayan kammala wa’adin mulkin sa.

Buhari zai sauka daga mulki a mako mai zuwa bayan kammala wa’adin mulkinsa na biyu inda zai mikawa Bola Ahmad Tinubu mulki a ranar 29 ga watan Mayu.

Jaridar Daily Trust ta gano cewa tuni masarautar Daura ta shirya gudanar da gagarumar Durbar domin girmama Buhari wanda ke rike da sarautar Bayajidda II.

Masarautar ta kuma shirya karin wasu wasannin da suka haɗa da Kokawa, Dambe da kuma Sharo.

Har ila yau wasu gamayyar kungiyoyi da suka haɗa da Daura Emirate Development Association (DEDA) suma sun shirya na su bikin domin tarbar Buhari a cewar Alhaji Aliyu Daura shugaban kungiyar ta DEDA.

Jami’an tsaro sun hana shiga ko kuma shiga gidan shugaban kasar.

More from this stream

Recomended