An sake mayar da Sheikh Daurawa a matsayin Shugaban Hisbah

Gwamnatin Jihar Kano karkashin Injiniya Abba Kabir Yusuf ta amince da naɗa Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa a matsayin babban kwamandan Hisbah na jihar.

A baya dai malamin ya taɓa riƙe hukumar, kuma hakan ya ba shi damar kawo canji wanda ya yi tasiri a jihar Kano

Ana ganin dawowar Malamin za ta taimaka wajen yaƙi da ayyukan alfasha da tabbatar da shika-shikan addinin Islama gami da muhimmin aikin da Kwamandan ya fara na auren zawarawa a faɗin jihar.

More from this stream

Recomended