An naɗa sabon shugaban kwalejin kimiyya da fasaha ta tarayya da ke Bauchi

Gwamnatin Najeriya ta naɗa Sani Usman a matsayin babban shugaban kwalejin kimiyya da fasaha ta tarayya da ke Bauchi a jihar Bauchi.

Ministan Ilimi, Adamu Adamu, ne dai ya mika wasikar nadin wa sabon wanda aka nada ɗin.

Har zuwa lokacin da aka nada shi a halin yanzu, Mista Usman ya kasance mataimakin shugaban makarantar ne, mukamin da ya rike daga 2018 zuwa 2022.



Nadin, a cewar mataimakin magatakardar hukumar mai kula da hulda da jama’a, Muhammad Rabiu, ya fara aiki ne daga ranar 21 ga watan Mayu.



Ya gaji Sanusi Waziri, wanda aka nada a watan Fabrairu, 2018.

More from this stream

Recomended