An matsa wa gwanatin Ganduje lamba ta yi dokar kare yara.

Kungiyoyim fararen hula a jihar Kano da ke arewacin Najeriya na ci gaba da matsin lambar neman gwamnatin Ganduje ta samar da dokar da za ta rika bin kadin hakkin kananan yara, biyo bayan sacewa tare da kashe Hanifa Abubakar da malamin makarantarsu Abdulmalik Muhammad Tanko ya yi.

Zainab Nasir na cikin wadanda suka yi wannan kiran kuma ta shaida wa manema labari cewa akwai bukatar a samar da wata cibiya ta neman karewa da kuma kwatar hakkin yara a Kano.

Ta kara da cewa a kuma rika bibiyar halin da makarantu masu zaman kansu suke ciki domin kaucewa kara faruwar irin wannan lamari, kuma wanda ake zargi da aikata wannan aiki a yi masa hukuncin da doka ta tanada.

Ta kuma ce jan kaar da ake yi wajen samar da wannan doka, yana kara bayar da damar aikata miyagun laifuka ga yara kanana kamar wanda aka shaida a yanzu, tana kuma shawartar gwamnati ta hanzartar zartar da wannan doka a matsayin almarin gaggawa.

More from this stream

Recomended