An kama wata mata da hodar ibilis tana kokarin tafiya kasar Saudiya

Hukumar NDLEA dake yaki da masu sha da kuma hana fataucin miyagun kwayoyi ta samu nasarar damke wata mata dauke da hodar ibilis a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Lagos.

Matar wacce bazawara ce an kama ta ne lokacin da take kokarin hawa jirgi domin zuwa kasar Saudiya.

Wani fefan da hukumar ta NDLEA ta fitar ya nuna yadda jami’an hukumar suka gano hodar ibilis din da matar ta boye a cikin kasan takalmi.

More from this stream

Recomended