Jami’an hukumar tsaro ta DSS a Kano sun kama daya daga cikin wadanda suka shirya garkuwa da mahaifiyar fitaccen mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara.Jami’an sun kuma kashe wani da ake zargi a wani samame na boye.
A cewar wata majiya, an kuma gano Naira miliyan 26.5 a yayin wannan aikin.
Majiyar ta ci gaba da cewa, rundunar ‘yan sandan jihar Kano bisa ingantattun bayanan sirri sun yi nasarar fatattakar ‘yan bindiga biyar a dajin Makarfi inda suke raba kudin fansa.
An kama mutumin da ake zargi shi ya kitsa sace mahaifiyar Rarara
