
Jami’an tsaron bijilante dake unguwar Gurungawa a karamar hukumar Kumbotso ta jihar Kano sun kama wasu mutane hudu da ake zargi da satar karnuka da kuma agwagwi.
Kwamandan bijilante na garin, Abdulhamid Dan-Azumi ya ce jami’ansa sun ji mostin mutanen da misalin karfe uku na dare lokacin da suka ji karnuka na haushi kuma wadanda da ake zargin sun samu nasarar kashe daya daga cikin karnuka.
Ya lissafa wadanda da ake zargi da suka hada da Sunusi Muhammad Abubakar, Sulaiman Baffa da Buhari Adamu, dukkaninsu mazauna unguwar Sheka da kuma Walid Ishak dake unguwar Gandun Albasa.
Kwamandan ya ce ” Bayan da muka kama su mun gano cewa sun dade suna aikata haka. Daya daga cikin su an san shi da satar kare yana turawa kudancin kasarnan.
“Mun kuma gano makamai a hannunsu za mu mika su hannun jami’an yan sanda.”