An Kalubalanci Masu Maganin Gargajiya a Najeriya

VOA Hausa

Gwamnatin Najeriya ta yi kira ga masana kimiyya da masu ruwa da tsaki da su gaggauta yin bincike domin gano maganin cutar coronavirus a cikin gida.

Sakataren gwamnatin tarayya kuma shugaban Kwamitin yaki da cutar ta COVID-19 Boss Mustapha ne ya bayyana hakan a wata hira ta musamman da ya yi da Muryar Amurka.

Kiran na zuwa ne bayan irin alkaluman da ke fitowa daga Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta NCDC wadanda ke nuna yadda ake samun hauhawar masu kamuwa da cutar a kullum.

Mustapha ya ce hauhawar adadin mutanen da ke kamuwa da cutar a fadin kasar a kullum ya sa aka fara daukan matakai na tuntubar kwararru da masana musamman ma masu maganin gargajiya na cikin gida.

Ya kara da cewa matakin har ila yau na nuna goyon baya ne da kara kwarin gwiwa domin su fito da basirar su ta kawo magungunan da suke da su saboda a gwada su a kimiyyance.

Sannan a tabbatar da sahihancinsu kafin a yi amfani da su.

Taskar bayanai da ke fitowa daga Hukumar Dakile yaduwar Cututtuka NCDC ta ce a yanzu an samu mutum kusan 6,000 masu dauke da cutar a Najeriya.

Dalilin kenan da ya sa gwamnati ta karbi tayin maganin da kasar Madagascar ta aiko da shi ta hannun Shugaban Guinea Bissau Oumaro Sissoco Embalo.

Amma hukumomin Najeriya sun ce ba za a fara amfani da maganin ba sai kwararru sun tabbatar ba shi da wata illa

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta yi kira da a yi gwajen-gwajen magungunan da ake samu kafin a fara amfani da su

More News

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye aikinsa na wani lokaci

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ya ajiye aikinsa na wani lokaci domin tunkarar matsalar lafiya.Mista Ngelale...

Ali Jita ya koma jam’iyar APC daga NNPP

Mataimakin shugaban majalisar dattawa dattawa, Sanata Barau Jibrin ya karɓi fitaccen mawakin Kannywood, Aliyu Isa Jita daga jam'iyar NNPP ya zuwa jam'iyar APC. Ali Jita...

An yi jana’izar mutumin da ya Æ™irÆ™iri tutar Najeriya

Iyalan marigayi, Pa Taiwo Akinkumi mutumin da ya ƙirƙiro tutar Najeriya sun yi bikin binne shi bayan da gwamnatin tarayya ta gaza cika alƙawarin...

‘Za a Æ™ara wa Æ´an bautar Æ™asa na NYSC alawus’

Babban daraktan hukumar yi wa kasa hidima ta kasa (NYSC) Birgediya Janar Yushau Ahmed, ya tabbatar wa ‘yan bautar kasar cewa za a kara...