An kai mummunan harin bam a kenya

An kona motoci da jikkata mutane da dama a harin Kenya

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

An kona motoci da jikkata mutane da dama a harin Kenya

Wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne ne sun kai wani mummunan hari a kan wani babban otel a birnin Nairobi, inda suka kashe mutane da dama.

An jiyo karar harbe-harbe da fashewar abubuwa a ginin otel din na DusitD2 da ke lardin Westlands, da wasu ofis-ofis ke ciki.

Kungiyar al-shabab ta Somalia ta ce ita ta kai harin.

‘Yan sanda sun kwashe mutane da dama cikin jini wadanda harin ya ritsa da su. A jiya Talata gwamnati ta ce ta tabbatar da tsaro a duk gine-gine da ke kasar.

An kai harin ne da misalin kafin 12 na rana agogon GMT. Dan bindigar ya jefa kunshi bam a cikin wata mota da aka ajiye a harabar shiga otel din, daya kuma ya tada bam din da ke jikinsa, kamar yadda shugaban ‘yan sandan kasar Joseph Boinnet ya shaida.

Wata mata da ke aiki a wani gini da ke makwabtaka da inda aka kai harin ta shaidawa kamfanin dilancin labaran Reuters cewa: ”Kawai na soma jin karan harbe-harbe, can kuma na soma ganin mutane na gudu wasu kuma na kokarin shiga cikin banki domin tsira da rayukansu.”

‘Yan sanda dai cikin hanzari suka nufi inda aka kai harin. Daya daga cikinsu ya shaidawa BBC cewa: ”Abubuwa sun kazanta. Mutane na matuwa.”

Da misalin karfe 8 na dare agogon GMT, Sakataren harkokin cikin gida Fred Matiang’i ya ce yanzu an tsaurara matakan tsaro a duk gine-ginen da ke yankin.

”Yanzu kura ta lafa kuma mun inganta tsaro a kasar mu, ” a cewar Sakataren. ”Ta’addanci ba zai taba samun gallaba a kan mu ba.”

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Bayan sa’a guda, an sake jiyo karan harbi daga yankin.

Har yanzu babu takamaiman adadin mutanen da harin ya ritsa da su. Sai dai wasu na cewa sun kidaya gawawaki biyar.

Kusan mutum 30 ke kwance a asibitin Nairobi inda suke karban kulawa, a cewar rahotannin kafafa yada labarai.

A ‘yan shekarun nan Kenya na yawan fuskantar hare-haren ta’addanci- musamman a yankunan da ke kusa da iyaka da Somalia da kuma birnin kasar.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Al-shabab ta yi ikirarin kai harin

More News

Najeriya za ta dena shigo da man fetur a cikin watan Yuni – Dangote

Aliko Dangote mutumin da ya fi kowa arziki a Nahiyar Afirka ya ce Najeriya za ta daina shigo da man fetur a cikin watan...

An ceto mutane 9 daga wani ginin bene da ya ruguzo a jihar Niger

Mutane 9 aka samu nasarar cetowa daga wani ginin bene mai hawa É—aya da ya ruguzo a yankin Sabon Gwari dake garin Minna babban...

An yi faÉ—a tsakanin masu sayar da waya da sojoji a kasuwar Abuja

Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, ta tura jami’an leken asiri zuwa kasuwar Banex – wata kasuwar kayan lantarki da na’urorin sadarwa da ke...

Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Wutar Da Wani Matashi Ya Cinnawa Wani Masallaci A Kano Sun  Karu Zuwa 16

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon wutar da wani ya cinnawa wani masallaci a ƙauyen Gadan a...