An hana baƙar fata aiki a cocin Turawa a Birtaniya

Augustine

Hakkin mallakar hoto
Augustine Tanner-Ihm

An ƙi amincewa da wani baƙar fata mai koyon aikin coci ko kuma son zama fasto sakamakon nuna wariyar launin fata daga shugabannin wata coci.

A wani saƙon email da aka tura masa domin mayar masa da martani dangane da takardar neman aikin da ya kai, an faɗa wa Augustine Tanner-Ihm cewa “ba lallai ya samu sakewa ba” idan aka ba shi aikin da ya nema a cocin.

A martanin da aka mayar masa ɗin, an ce duk da ƙwarewarsa, babu amfani a ci gaba da dogon bayani dangane da batun neman aikinsa a kudancin Ingila.

Cocin Ingilar ta ba shi haƙuri.

Mista Tanner-Ihm wanda ɗan asalin Chicago ne, mai muƙamin Rabarand ne a Amurka, kuma ya nemi a ba shi aiki a wata coci a kudancin Ingila.

Mista Tanner-Ihm mai shekaru 30, yana karatu ne a Jami’ar Durham kuma ya ce ya zuciyarsa ta yi ƙuna a watan Fabrairu bayan ya samu amsa daga cocin da ya nemi aiki.

“A matsayina na ɗan Afrika daga Chicago, wanda iyayena na kakannina suna da rai lokacin gwagwarmayar neman ‘yanci, na yi zaton babu ruwan launin fatata da aikina na coci,” in ji shi.

“Ina tunanin cocin na da alaƙa da wariyar launin fata.”

Rabarand Goldsmith wanda darakta ne a cocin Ingila ya bayyana cewa: “Muna ɗaukar duk wani zargi da muhimmanci, har cewa an hana mutum wani muƙami saboda ƙabilarsa.”

Ya bayyana cewa ɗaya daga cikin mambobinsa sun nemi Mista Tanner domin jin abin da ya faru, ya ƙara da cewa: “Mun sa wanda ya yi masa hakan ya rubuta masa takarda a rubuce domin ba shi haƙuri”.

More from this stream

Recomended