Mutane 6 ne suka rasa rayukansu a wata arangama da aka yi tsakanin ‘yan bindiga da ’yan banga da aka fi sani da ‘Yan Sakai a karamar hukumar Gada a jihar Sakkwato.
‘Yan bangar, a cewar wata majiya a yankin da ta nemi a sakaya sunanta saboda yadda lamarin ya kasance, an ce sun dauki fansa ne kan kisan da wasu ‘yan bindiga suka yi wa shugabansu, Alhaji Dahiru.
Shaidun gani-da-ido sun ce rikicin ya fara ne a lokacin da wani jagoran ‘yan banga kauyen Gidan Hashimu ya yi wani yunkuri na kama wasu barayin shanu.
Rahotanni sun ce ‘yan bindigar da ake zargin, a daidai lokacin da rikicin ya yi kamari, sun harbe shugaban ‘yan bangan har lahira, lamarin da ya janyo ramuwar gayya daga ‘yan banga.
Daya daga cikin shaidun gani da ido ya ce kafin isowar tawagar jami’an tsaron kasuwar, sama da mutum shida ne suka mutu.