An gudanar da zanga-zanga kan ƙarancin takardi kuɗi da man fetur

0

Wasu matasa sun gudanar da zanga-zanga tare da kone-kone a jihar Ogun kan ƙarancin sabbin takardun kuɗin naira da kuma ƙarancin man fetur.

An shafe watanni dai ana fama da matsalar ƙarancin man fetur a sassa daban-daban na kasar nan abin da yake haifar da dogayen layuka a gidajen mai.