An ga jinjirin watan Shawwal na shekarar Hijira ta 1444.

An bayyana hakan ne a cikin wata ‘yar gajeriyar sanarwa ta shafin sada zumunta na Facebook na Haramain Sharifain.
Sanarwar ta ce, “An ga jinjirin watan Shawwal 1444 a yau a Tumair da Sudair wanda ya nuna cewa gobe Juma’a, 21 ga Afrilu, 2023 ita ce ranar Eid Al Fitr.”
Wannan ne ya kawo karshen azumin watan Ramadan.
