An dawo da zirga-zirgar jiragen sama a filin jirgin saman Kaduna

Bayan dakatarwar watanni 19 saboda dalilan tsaro dake da alaka da yan bindiga zirga-zirgar jiragen saman Hassan Usman Katsina dake Kaduna.

Saukar jirgin saman kamfanin Air Peace kirar ERJ-145 wanda ya sauka a filin jirgin da karfe 05:10 na yamma shi yake nuna dawowar cigaba da zirga-zirgar jiragen sama a filin jirgin.

Idan za a iya tunawa a cikin watan Maris na shekarar 2022 a ka samu hare-haren yan bindiga a yankin dake kusa da filin jirgin har ya jawo an dakatar da zirga-zirga ta wucin gadi kafin daga baya jirgin kamfanin Azman ya dawo cigaba da zirga-zirga a filin jirgin.

Hakan ya tilastawa fasinjoji masu zuwa Kaduna daga Lagos su sauka a Abuja ko Kano sannan su hau mota zuwa Kaduna.

Manajan filin jirgin, Adamu Sheikh wanda ya bayyana cewa kamfanonin jiragen sama da dama na shirye-shiryen sake fara fara zirga-zirga a filin jirgin inda ya jaddada aiwatar da tsauraran matakan tsaro domin sauka da kuma tashin jiragen sama.

More from this stream

Recomended