An dage kididdigar yawan jama’a ta 2023, wadda aka shirya gudanarwa tun daga ranar 3 zuwa 7 ga Mayu, 2023, kuma gwamnati mai zuwa za ta tsayar da wata sabuwar rana.
Gwamnatin Tarayya ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ma’aikatar yada labarai da al’adu ta fitar ta shafinta na Twitter.
Sanarwar ta ce, “Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da dage kididdigar yawan jama’a da gidaje na shekarar 2023, wanda tun farko aka shirya gudanarwa daga 3-7 ga Mayu 2023, zuwa ranar da gwamnati mai zuwa za ta tsayar da rana.
“Shugaban ya amince da hakan ne bayan ganawa da wasu mambobin majalisar zartarwa ta tarayya da shugaban @natpopcom da tawagarsa a fadar shugaban kasa da ke Abuja ranar Juma’a 28 ga Afrilu 2023.”