Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasiru Elrufai ya samu sarautar gargajiya ta Gbobaniyi na kasar Ijebu dake jihar Ogun.
Oba Sikiru Kayode Adetona, shi ne ya bawa, Elrufai sarautar a wani biki da aka gudanar a ranar Asabar.
Elrufai shi ne mutum na farko daga yankin arewacin Najeriya da masauratar ta Ijebu ta bawa sarauta.


