A ranar Talata ne Iran ta ayyana hutun kwanaki biyu ga ma’aikatan gwamnati da kuma bankunan kasar baki daya, a daidai lokacin da yanayin zafi ke kara kamari a fadin kasar, in ji kafar yada labaran kasar.
An yanke shawarar ne bayan da ofishin hasashen yanayi ya yi hasashen yanayin zafi sama da digiri 40 (Fahrenheit 104) a birane da dama, da kuma kusan ma’aunin Celsius 50 (122 Fahrenheit) a kudu maso yammacin kasar.
Kamfanin dillancin labaran IRNA ya nakalto kakakin gwamnatin kasar Ali Bahadori Jahromi na cewa, majalisar ministocin kasar ta amince da kudirin ma’aikatar lafiya na ayyana ranakun Laraba da Alhamis a ranakun hutu a duk fadin kasar domin kare lafiyar jama’a.
Ya ce an dauki matakin ne saboda “zafin da ba a taba gani ba” ya mamaye kasar.