Amfani da wutar lantarki don magance ‘cutar’ luwadi | BBC Hausa

Dr Tommy Dickinson

Hakkin mallakar hoto
Dr Tommy Dickinson

Image caption

Dakta Tommy Dickinson ya ce an daina amfani da wannan tsarin na jona wutar lantarki don karkatar da hankalin mutum tun shekarun 1970 a Burtaniya

“Daga farko an jona min wayoyin lantarki a tafin kafata.

“Wutar lantarkin na ja na bayan dakika 15 zuwa 30.”

An yi amfani da wani tsari na karkatar da hankalin John (ba sunansa na gaskiya ba) ta hanyar sa masa wutar lantarki a Jami’ar Queen’s da ke Belfast lokacin da yana dalibi a shekarun 1960. An nuna masa hotunan maza tsirara sannan aka sa wayoyin lantarki suka ja shi idan hotunan suka motsa masa sha’awa.

Wani mai magana da yawun jami’ar ya bayyana nadama bisa amfani da wannan tsarin.

John ya girma a shekarun 1950s a wani kauye a arewacin Ireland.

“Cocin da nake zuwa na Presbyterian ne, don haka na shiga tsaka mai wuya da na gane cewa ni dan madugo ne,” ya shaida wa BBC.

“A lokacin da nake da shekara 15, na fahimci cewa ina cikin mutanen nan da ke sha’awar ‘yan uwana maza kuma al’umarmu ba ta na’am da hakan don haka na shiga rudani.

John ya fara magana ne da likitansa, wanda ya tausaya wa John sannan ya shirya masa tattaunawa da mai bayar da shawarwari a wani asibiti.

Sai dai lokacin da ya je jami’ar Queens a matsayin dalibi a karshen shekarun 1960, an tura shi bangaren kula da lafiyar kwakwalwa na jami’ar.

“Na yi farin ciki da duk abubuwan da suka gaya min, waraka kawai nake nema,” a cewarsa.

Manufar tsarin amfani da lantarki wajen karkatar da hankali, shi ne don ya rika hada sha’awarsa ta saduwa da maza ‘yan uwansa da azabar da yake ji idan lantarkin ya ratsa jikinsa.

“An nuna min hotunan wasu samari tsirara,” in ji John.

“An jona min wasu wayoyi da ke da wutar lantarki a jikinsu a tafin kafafuwana, sai su ja ni.

“Babu mamaki, wannan lamari ne mai muni a gare ni saboda ina da saurin jin zafi a tafukan kafafuna amma na yi kokarin shawon kansu su sa min lantarkin a hannuwana.

“Don haka sai suka daura min wani abin a hannuna wutar ta ja ni a nan.”

‘Abu ne mai muni’

John na latsa wani maballi idan sha’awa ta motsa masa bayan kallon hotunan mazan.

“Idan na latsa maballin hakan na nufin na ji sha’awa kenan, don haka bayan dakika 15 ko 30 idan ban sake latsa maballin ba sai su sa wutar ta ja ni,” ya ce.

“Sai su ci gaba da sa min lantarki har sai na latsa maballin don sanar da su cewa sha’awar ta gushe min.

“Kwarai akwai azaba, yana da ciwo.

“Hakan na nufin a duk lokacin da kwakwalwata ta ji sha’awar saduwa da namiji sai ta tuna wannan azaba da aka gana min.”

An kuma karfafa wa John gwiwa ya nemi mata a lokacin da ake masa wannan salon neman warakar.

A wani bincike da aka buga a mujallar Ulster Medical Journal a 1973, malamai a banagren lafiyar kwakwalwa da halayyar dan Adam a jami’ar Queens da ke Belfast sun ce ba a cika amfani da wutar lantarki wajen karkatar da hankali ba a wannan matakin.

Amma duk da haka suna amfani da shi.

Babu shaidar cewa tsarin ya yi aiki

“Muna mayar da hankali kan tsare-tsaren da ake amfani da su wajen sauya tunanin mazan da ke sha’awar maza don su fara sha’awar mata,” a cewarsu.

“Asali ma ba mu cika amfani da wutar lantarki ba, musamman ma a matakin farko.”

A cewar Dakta Tommy Dickinson – shugaban sashen lafiyar kwakwalwa a Kwalejin King’s dake Landan- wannan tsarin amfani da wutar lantarki bai samu karbuwa ba a Burtaniya.

“Duk da cewa kyauta ake yin tsarin, an yi kiyasin cewa kusan mutum 1,000 ne kawai suka taba shiga tsarin samun warakar,” a cewarsa.

“Babu wata shaida dake nuna cewa wannan tsarin ya yi aiki,” Ya shaida wa BBC.

“Shaidar kawai da na samu ita ce wannan salon na mummunar tasiri a rayuwar mutane.”

Dakta Dickinson ya ce gaba daya an daina amfani da wutar lantarki don magance madigo.

“Babban abin da ya janyo raguwar amfani da wadannan tsare-tsare shi ne karuwar kungiyoyin kare hakkin ‘yan luwadi da madigo da kuma ‘yan madigon maza da mata da suka yi fatawali da tunanin cewa wata cuta ce ke damunsu,” ya ce.

Hakkin mallakar hoto
PAcemaker

Image caption

Dubban mutane sun halarci taron ‘yan madigo da luwadi a Belfast a 2019

Wani mai magana da yawun jami’ar Queens dake Belfasr ya ce makarantar ta yi nadamar amfani da irin wannan salon a wasu lokuta.

“Babu wata kwakkwarar shaida dake nuna cewa wannan tsarin na gyara tunanin ‘yan madugo,” a cewarsa.

“Jami’ar Queens da NHS ta dade bata goyon bayan amfani da wannan tsarin.

“Duk da cewa ba za mu iya sauya abin da muka yi a baya ba, Jami’ar Queens a shirye take ta samar da yanayi mai cike da goyon baya.”

Daga karshe, John ne da kansa ya yanke shawarar dakatar da tsarin da ake masa a jami’ar Queens.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

An tura John neman magani a Jami’ar Queens

“Bayan ‘yan shekaru na kokarin na samu waraka sai na gane cewa tsarin ba ya aiki. Sha’awar da nake yi wa maza na nan kuma bana sha’awar mata kamar yadda nake sha’awar maza,” a cewarsa.

“Bana jin abin ya shafi rayuwa ta, ban fuskanci kunci ba daga baya.

“Na yi sa’a, ba a dade ba na fara haduwa da mutane iri na masu sha’awar maza kuma hakan ya sauya rayuwata gaba daya.

“Ban san yadda mutane za su ji da wannan labarin ba.

“A lokacin ban yi tunanin dabbancin abin ba, amma yanzu hakan ya sauya.”

More News

Mayaƙan Boko Haram Biyu Sun Miƙa Kansu Ga Sojoji

Aƙalla mayaƙan Boko Haram biyu ne suka miƙa kansu ga dakarun sojan Najeriya na rundunar Operation Haɗin Kai a yankin gabashin jihar Borno. Mayaƙan biyu...

Isa Dogonyaro ĆŠan Majalisar Tarayya Daga Jihar Jigawa Ya Rasu

Isa Dogonyaro wakilin al'ummar ƙananan hukumomin Garki da Baɓura a majalisar wakilai ta tarayya ya rasu. Ɗaya daga cikin abokan aikin marigayin a majalisar tarayya,...

Zargin badaƙala: Kotu ta hana Hadi Sirika fita ƙasar waje

A ranar Alhamis ne babbar kotun birnin tarayya Abuja ta hana tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, diyarsa Fatimah da sirikinsa Jalal Hamma...

Kotu ta bayar da belin Hadi Sirika da Ć´arsa

Wata babbar kotun tarayya dake Abuja ta bayar da belin tsohon ministan harkokin sufurin jiragen sama, Hadi Sirika da kuma wasu mutane uku kan...