
Mazauna kusan gidaje sama da 100 ne ambaliyar ruwa ta raba da gidajensu a unguwannin Rikkos, Bauchi Road, Anguwan Rogo da kuma Naraguta dake karamar hukumar Jos North.
An samu ambaliyar ruwan ne biyo bayan mamakon ruwan sama da aka samu a ranar Asabar da kuma Lahadi.
Wani mazaunin Bauchi Road mai suna Tanko Aliyu ya fadawa manema labarai cewa ba a samu asarar rayuka a ambaliyar ba amma kuma ta raba mutane da dama da gidajensu inda a yanzu suke zaune tare da yan uwansu.
Salamatu Aliyu É—aya daga cikin waÉ—anda abun ya shafa ta bayyana cewa basu taba tsammanin ambaliyar ruwan za ta faru ba har ta kai ta raba ta gidanta ita da makociyarta dake Anguwar Rogo inda tayi kira ga gwamnati kan ta kawo musu dauki.