al-Bashir ya ce Yariman Saudia ne ya ba su kudin da aka kama | BBC Hausa

Omar al-Bashir

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Omar al-Bashir na halartar zaman kotun ne a cikin keji

A yayin zaman shari’ar alkalin kotun da aka gabatar da tsohon shugaban na Sudan, Omar al-Bashir, ya sheda masa cewa an samu tarin kudaden waje da na kasar da yawansu ya kai dala miliyan takwas a gidansa.

Mai shari’ar ya tuhumi dadadden shugaban na Sudan mai shekara 75 da mallaka da kuma amfani da kudin ta haramtacciyar hanya, abin da shi kuma ya musanta.

A lokacin da alkalin yake masa tambayoyi a karon farko, a karo na uku da yake bayyana a kotu, al-Bashir ya ce Yariman Saudiyya, Mohammed bin Salman ne ya turo masa kudin dala miliyan 25.

Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Omar al-Bashir ya gaisawa da magoya baya da ‘yan uwansa

Ya ce ba wai ya yi ko yana amfani da kudin ba ne don amfanin kansa, ya ce ajiye kudin da ya yi a gidansa karramawa ce ga Yariman na Saudiyya domin shi ya bukaci hakan:

Ya ce: ”Ba mu kai kudin Babban Bankin Sudan ba saboda muna son sirrin ta inda kudin suka fito ne, kuma mun yi hakan ne domin abin da, Yariman ya bukaci a yi kenan.

Ya kara da cewa: ”Kuma da zan so a ce wannan kotu ce da ke zamanta a sirri, domin kada a bayyana sunan Yariman. Saboda ba ya son sunansa ya bayyana a ko ina, abin da ya sa ya aiko da kudin kenan a wani jirgi na daban da kuma jakada na musamman. Wannan shi ne abin da ya so, don kada a san inda ya fito.”

Wani mai bincike ya gaya wa kotun da ke shari’ar a Sudan cewa tsohon shugaban ya amince da karbar kudin, miliyoyin dala daga Saudiyya, amma lauyoyinsa sun ce tuhumar da ake ma sa ba ta da tushe.

A watan Afrilu ne aka hambarar da shugaban bayan wata da watanni na zanga-zanga, abin da ya kawo karshen mulkinsa na kusan shekara talatin.

Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

An shafe wata da watanni ana zanga-zanga a kasar ta Sudan

A watan Yuni ne na wannan shekara ta 2019, masu gabatar da kara suka ce sun gano wasu buhuna makare da kudaden kasar waje a gidansa.

Sauran tuhume-tuhume da ake yi wa tsohon shugaban sun hada da haddasa rikici ta hanyar harzuka jama’a da kuma hannu a kisan masu zanga-zanga.

Zarge-zargen sun taso ne daga binciken kisan da ake yi na wani likita da aka kashe lokacin zanga-zanga wadda ta yi sanadiyyar zuwan karshen mulkin na al-Bashir.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Masu rajin mulkin dumokuradiyya na Sudan sun cimmma babbar nasara bayan da sojoji suka amince da yarjejeniyar da za ta kai ga kafa mulkin farar hula

Majalisar mulkin kasar ta soji wadda ta karbi mulki bayan kawar da al-Bashir ta kulla yarjejeniya da ‘yan hamayya na farar hula, yarjejeniyar raba iko, wadda za ta kai ga kafa mulkin farar hula a karshe.

Wannan matakin ne ya kai ga karshen tashin-tashinar da ake ta yi bayan gwamnatin ta Mista Bashir.

More News

Tsoffin gwamnoni sun wawashe sama da naira tiriliyan 2 tun komawa dimokuraÉ—iyya

Aƙalla tsoffin gwamnoni 58 ne ake zargin sun wawure kuma sun yi almubazzarancin jimillar naira Tiriliyan 2.187 a cikin shekaru 25 tun komawa mulkin...

Ƴan sanda sun kama mutane 50 kan rikicin da ya faru a wata kasuwa a Lagos

Rundunar Æ´an sandan jihar Legas ta kama mutane sama da 50 da ake zargin suna da hannu rikicin da ya faru a kasuwar Ile...

Ƴan Sanda sun kama wanda ya shirya kai harin jirgin ƙasar Abuja-Kaduna a shekarar 2022

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce jami'anta sun kama wani mutum mai suna Ibrahim Abdullahi wanda ake zargi da kitsa harin jirgin ƙasar da...

Ƴansanda sun kama wanda ya kitsa harin da aka kai wa jirgin ƙasa a Kaduna

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a ranar Alhamis, ta sanar da kame wanda ake zargin ya shirya harin da aka kai a jirgin ƙasan Abuja-Kaduna...