Akwai bukatar a sake sauya tsarin zaben Najeriya – EU | BBC Hausa

Tawagar Tarayyar Turai a zaben Najeriya

Hakkin mallakar hoto
@inecnigeria

Tawagar Tarayyar Turai da ta sa ido a zaben Najeriya ta ce akwai bukatar a sauya tsarin zaben kasar bayan gano wasu matsaloli a zabukan 2019 da aka gudanar.

Tawagar ta Tarayyar Turai ta fadi haka ne lokacin da take gabatar da rahotonta na karshe kan zabukan shugaban kasa da na ‘yan majalisa da gwamnoni da aka gudanar a 2019.

Babbar jami’ar da ta jagoranci tawagar Maria Arena ta ce an lalata gaskiyar tsarin zaben Najeriya na 2019 saboda rikici da tsoratarwa.

Ta ce an samu matsaloli da suka shafi tsaro da matsalar kai kayan zabe da kuma rashin fitowar jama’a.

Daga cikin shawarwarin da rahoton ya bayar, sun hada da inganta tsarin tattara sakamakon zabe, musamman tsarin da zai bayyanawa jama’a sakamakon kafin sanar da shi.

Babu dai wani martani da ya fito daga bangaren hukumomin Najeriya game da rahoton na Tarayyar Turai.

Rahoton na zuwa bayan watanni uku da aka gudanar da zaben shugaban kasa wanda shugaba Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC ya lashe.

Tarayyar Turai ta dora laifin matsalolin da aka samu akan jam’iyya mai mulki, kan rashin tsawatarwa ga magoya bayanta da rashin daukar matakan kaucewa cin karo da matsalolin.

Ta ce an yi amfani da karfin mulki a bangarorin Tarayya da jiha.

Kuma dakatarwar da aka yi wa Alkalin alkalan kasar, makwani kafin a gudanar da zabe ya saba wa ‘yancin shari’a a Najeriya.

Dan takarar babbar jam’iyyar adawa ta PDP Alhaji Atiku Abubakar ya shigar da kara kotu inda yake kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa.

Tarayyar Turai ta bukaci a gaggauta sauya tsarin zaben Najeriya saboda matsalolin da ta gano kafin zaben 2023.

More News

Najeriya za ta dena shigo da man fetur a cikin watan Yuni – Dangote

Aliko Dangote mutumin da ya fi kowa arziki a Nahiyar Afirka ya ce Najeriya za ta daina shigo da man fetur a cikin watan...

An ceto mutane 9 daga wani ginin bene da ya ruguzo a jihar Niger

Mutane 9 aka samu nasarar cetowa daga wani ginin bene mai hawa É—aya da ya ruguzo a yankin Sabon Gwari dake garin Minna babban...

An yi faÉ—a tsakanin masu sayar da waya da sojoji a kasuwar Abuja

Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, ta tura jami’an leken asiri zuwa kasuwar Banex – wata kasuwar kayan lantarki da na’urorin sadarwa da ke...

Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Wutar Da Wani Matashi Ya Cinnawa Wani Masallaci A Kano Sun  Karu Zuwa 16

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon wutar da wani ya cinnawa wani masallaci a ƙauyen Gadan a...