Akwai Æ™arancin haihuwa tsakanin ma’aurata, in ji WHO

Mace mai ciki

Asalin hoton, Getty Images

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta yi kiran a dauki matakin gaggawa kan magance ƙaruwar matsalar rashin haihuwa.

A wani sabon rahoto da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta fitar, ta ce sama da É—aya bisa shida na baligai ne ke gaza samun haihuwa a wani mataki na rayuwarsu.

Daraktar fannin bincke kan lafiyar ma’aurata da haihuwa a hukumar, Pascale Allotey ta ce akwai Æ™arancin kula da fannin rashin haihuwa.

WHO ta ce akwai buÆ™atar a gaggauta bijiro da hanyoyin samar da waraka ga matsalar rashin haihuwa tsakanin ma’aurata.

Sabon rahoton na cewa sama da ma’aurata guda cikin shida na fama da matsalar haihuwa a rayuwarsu.

Binciken ya kuma nuna rashin daidato tsakanin rukunin masu arziki da karamin karfi.

Ƙarin labarai:

Pascale Allotey ta ce akwai ƙarancin kulawa kan batun haihuwa a wannan lokaci.

Ta ce adadin da ake samu na ma’aurata dake fama da matsalar haihuwa na nufin akwai damuwa, tare da buÆ™atar inganta hanyoyin tunkarar wannan matsala.

Da kuma gano musababbi da maganin matsalar.

A cewarta abu ne da kusan ba a bai wa fifiko da kyau, galibi mutane ba sa samun abin da suke so.

Hakan na nufin mutanen da ke neman taimako kan ƙare cikin uƙuba da kashe kuɗin da ya wuce kima.

Koda a ce wannan tsari akwai shi to ba kowa ke iya biya ba saboda tsadarsa.

Shugaban Hukumar lafiya ta dunya, Dakta Tedros Adhanom Ghabrayesus ya ce bincikensu ya huna musu cewa wannan ba matsalar da za a zura wa ido ba ne.

Ya kuma yi kira ga gwamnatocin ƙasashe da su riƙa bayar da fifiko domin masana su inganta bincike a kuma bijiro da tsare-tsare cikin sassauci.

More News

Gwamnatin Adamawa Ta Ƙara Hutun Ɗaliban Makarantu Saboda Annobar Cutar Ƙyanda

Gwamnatin jihar Adamawa ta tsawaita lokacin komawar É—aliban jihar makarantunsu domin fara  zangon karatu na uku saboda annobar cutar Æ™yanda. A wata sanarwa ranar Litinin,...

Sojan Jamhuriyar Nijar sun kama Gawurtaccen ÆŠan Fashin dajin Najeriya Kachalla Mai Daji

Dakarun sojan Jamhuriyar Nijar sun samu nasara kama gawurtaccen É—an fashin dajin nan mai suna Kachalla Mai Daji a garin Illela dake kan iyakar...

Ƴan Fashin Daji Sun Kashe Mutane 7 A Jihar Kebbi

Mutane 7 aka bada rahoton ƴan fashin daji sun kashe  a garin Tudun Bici dake ƙaramar hukumar Danko Wasagu ta jihar Kebbi. A cewar mazauna...

Tsoffin gwamnoni sun wawashe sama da naira tiriliyan 2 tun komawa dimokuraÉ—iyya

Aƙalla tsoffin gwamnoni 58 ne ake zargin sun wawure kuma sun yi almubazzarancin jimillar naira Tiriliyan 2.187 a cikin shekaru 25 tun komawa mulkin...