Aisha Yesufu: Tarihin matar da ke zanga-zangar SARS sanye da hijabi

Bayanan bidiyo,
Aisha Yesufu: Matar da ke zanga-zangar SARS sanye da hijabi

Matakin da rundunar ‘yan sandan Najeriya ta dauka na rusa sashenta da ke yaki da fashin da makami, wanda aka fi sani da SARS a takaice, ya sanya ‘yan kasar murna matuka.

Gabanin wannan mataki, ‘yan Najeriya sun kwashe shekara da shekaru suna fafutukar ganin an rusa rundunar SARS, wadda ake zargi da cin zarafi da azabtarwa da ma kashe mutanen da ta kama.

Sai dai wani muhimmin abu da ya fito fili tun bayan rusa SARS shi ne irin rawar da masu fafutuka suke takawa wurin kawo sauyi a duniya.

Aisha Yesufu na cikin mutanen da suka kwashe shekara da shekaru suna fafutukar ganin an samar da mulki na gari a Najeriya, kuma sunanta ya kara fitowa fili a lokacin da ta shige gaba wajen fafutukar ganin an ceto ‘yan matan makarantar Chibok da mayakan Boko Haram suka sace a 2014.

A wannan karon ma, ta taka muhimmiyar rawa a zanga-zangar kyamar SARS inda wani hotonta da ta bijirewa ‘yan sanda ya karade shafukan intanet na kasar.

Wani abu da ya bambanta ta wajen wannan fafutuka shi ne yadda ake saukin gane ta saboda ko da yaushe tana sanye da hijabi.

Wace ce wannan mata da ke son kawo sauyi a Najeriya?

An haifi Aisha Yesufu a 1973 a birnin Kano da ke arewacin Najeriya kuma a birnin ta girma.

‘Yar asalin jihar Edo da ke kudu maso kudancin kasar ce.

Ta yi karatunta na Digiri a Jami’ar Bayero da ke Kano a fannin Microbiology.

‘Yar fafutukar tana da aure da ‘ya’ya.

“Ina bala’in son mijina,” a cewar Aisha wadda ta kara da cewa mijinta ba ya zuwa wurin da take fafutuka saboda shi ba mai son hayaniya ba ne.

More News

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...

Yadda rikici a kan gishirin N20 ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a Kano

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun kanen matarsa, wani Magaji Salisu saboda gishirin N20. Dan marigayin,...

Sojoji Sun Kashe Mayaƙan IPOB 5

Dakarun rundunar sojan Najeriya da kuma ta rundunar sojan ruwan Najeriya a ranar Talata sun kashe mayaƙan ƙungiyar IPOB guda biyar a yayin musayar...

ÆŠan agajin Izala ya samu lambar yabo, kujerar hajji, kyautar mota bayan ya tsinci naira miliyan 100 ya mayar wa mai su

Salihu AbdulHadi Kankia, mamba ne na kungiyar agaji ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS), ya samu yabo da tukuicin mayar da...