Aikin Hajji: ‘Za ku iya fara tanadin kuɗin aikin Hajji da naira 1000’

..

Hukumar alhazai ta Najeriya ta fito da bayanai game da sabon tsarinta na adashen gata ga dukkan masu buƙatar zuwa Hajji a nan gaba ta hanyar biyan kuɗin kujera da kaɗan-kaɗan.

Ta wannan tsari ne hukumar ta saka hannu kan wata jarjejeniya da Bankin Jaiz a Abuja babban birnin tarayyar ƙasar.

Dakta Aliyu Tanko, shi ne jagoran wannan sabon tsari na adashen gata a hukumar alhazai ta Najeriya, inda ya ce wannan tsarin wata hanya ce ta buɗe wa duk wanda yake Musulmi, ko talaka ko mai kuɗi domin zuwa aikin Hajji.

“Wannan tsari ne da zai bayar da dama ga mutum ya rinƙa ajiye kuɗi a hankali, mai dubu ɗaya ya je ya ajiye, mai dubu biyar ya je ya ajiye, wanda ke da dubu goma shi ma ya je ya ajiye,” in ji Dakta Aliyu.

“Wannan kuɗin da kowa ya ajiye, shi ne za a haɗa su kuma a rinƙa juyawa a harkoki na kasuwanci waɗanda suke halal, ana samun riba ana haɗawa da uwar kuɗi har zuwa lokacin da ainahin mai ajiya ɗin abin da ya ajiye zai ishe shi biyan kuɗin Aikin Hajji.”

Alhaji Abubukar Sarkin Fawa Dambo, shi ne shugaban hukumar alhazai ta Najeriya kuma shugaban shugabannin hukumomin alhazai na Najeriya kuma ya shaida wa BBC cewa wannan shiri da aka ɓullo da shi ya kamata a yi maraba da shi.

Ya kuma ce idan mutum ya ɗauki lokaci mai tsawo yana tara waɗannan kuɗaɗe, ribar da mutum ya samu daga kudinsa da aka juya ta hanyar halal za ta kawo masa sauƙin cikon kuɗin da ya kamata ya yi.

Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya, ta ɓullo da wannan tsari ne na adashen gabata, domin kawo sauƙi ga dukkan mai niyyar sauke farali acikin dogo ko matsakaicin lokaci.

(BBC Hausa)

More News

Ƴan sanda sun kama mutane 50 kan rikicin da ya faru a wata kasuwa a Lagos

Rundunar ƴan sandan jihar Legas ta kama mutane sama da 50 da ake zargin suna da hannu rikicin da ya faru a kasuwar Ile...

Ƴan Sanda sun kama wanda ya shirya kai harin jirgin ƙasar Abuja-Kaduna a shekarar 2022

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce jami'anta sun kama wani mutum mai suna Ibrahim Abdullahi wanda ake zargi da kitsa harin jirgin ƙasar da...

Sojoji Sun Ceto Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin tabbatar da tsaro a jihar Filato da wani ɓangare na jihar Kaduna sun samu nasarar ceto mutane...

Matatar Mai Ta Kaduna Za Ta Fara Aiki A Ƙarshen 2024

Kamfanin Kaduna Refining and Petrochemical Company KPRC ya ce matatar mansa za ta fara aiki a shekarar 2024. Mustapha Sugungun managan matatar man ta KRPC...