Rundunar ‘yan sandan jihar Abia ta tabbatar da mutuwar wata mata mai bishara mai suna Happiness Echieze a wani gidan otel na Aba, inda aka ce ana zargin kashe ta aka yi.
Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da wasu kafafen yada labarai na yanar gizo a jihar suka yi ikirarin cewa matar mai wa’azin ta mutu ne a gidan baki a lokacin da ake zarginta da yin lalata da wani babban bishof na cocin Pentecostal, Bishop Timothy Otu.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin a ranar Alhamis, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Abia, ASP Maureen Chioma Chinaka, ya ce a ranar 13 ga watan Agusta, wani Mista Godwin Akapan da ke zaune a otel na Jubilee da ke kauyen Ovom a karamar hukumar Obingwa ya kai rahoto ga ofishin ‘yan sanda na Isialangwa game da lamarin da ya faru.
A cewar sanarwar ‘yan sandan, “An bayyana cewa a yammacin ranar 12 ga watan Agusta, 2023, da misalin karfe 09:25 na dare, wani limamin coci mai suna Timothy Otu (namiji) da ke da alaka da Agape Evangelical Ministry da ke Junction Obikabia a karamar hukumar Obingwa, ya shiga otel ɗin tare da wata mata mai suna Happiness Echieze (mace) daga karamar hukumar Isialangwa, jihar Abia. Happiness Echieze mai shekaru 43 a duniya.
“Karin bayani da Mista Akpan ya bayar ya nuna cewa a wannan ranar, da misalin karfe 12:00 na safe ya shiga dakin otal din limamin cocin da aka ambata a baya ya gano gawar Happiness Echieze da ba ta da rai. An same ta ba tufa, wani farin abu ne ke fitowa daga bakinta da hancinta. Abin takaici, limamin ba ya nan a wurin,” in ji ‘yan sandan Abia.