Abin da ya sa Buhari ya ki tsoma baki a rikicin Ganduje da Sarki Sanusi II | BBC Hausa

Gwamna Ganduje da Sarki Sanusi II
Hakkin mallakar hoto
Kano government
Image caption

Gwamna Ganduje da Sarki Sanusi II sun dade suna kai ruwa rana

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya bayyana dalilan da suka sanya shi kin tsoma baki a rikicin gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.

Gwamna Ganduje da Sarki Sanusi II sun kwashe tsawon lokaci suna tafka rikici, lamarin da ya kai ga raba masarautar Kano zuwa masarautu biyar– wadanda suka hada da sarautar Rano da ta Karaye da ta Bichi da ta Gaya, baya ga sarautar cikin kwaryar Kano ta Sarki Sanusi II.
Wannan lamari dai ya raba kawunan mazauna jihar har ta kai ga masu zaben Sarki a jihar sun kai gwamnatin Ganduje kotu kan batun.
Kazalika wasu kungiyoyin dattawan jihar da ma na arewacin Najeriya, da tsoffin shugabannin kasar sun sanya baki a cikin rikicin, wanda ya ki ci ya ki cinyewa.
Sai dai duk da tabarbarewar lamarin, Shugaba Buhari bai fito fili ya tsoma baki ba, ko da yake wasu majiyoyi sun ce fadar shugaban kasar karkashin jagoracin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, ta rika kai gwauro tana kai mari kan batun.

  • Hotunan ziyarar Kanawa zuwa wajen Shugaba Buhari
  • Abubuwa 5 da Sarki Sanusi II ya fada da ya ziyarci Ganduje

Amma wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta aike wa manema labarai ranar Juma’a, bayan shugaban ya gana da wata tawagar al’umar Kano da ‘yan jam’iyyar APC wacce Gwamna Ganduje ya jagoranta zuwa fadarta Shugaba, ta bayyana dalilan da ska sanya Shugaba Buhari bai tsoma baki kan rikicin ba.
‘Kundin tsarin mulki ya hana ni yin magana’
Mai magana da yawun shugaban kasar Malam Garba Shehu ya ambato Shugaba Buhari yana cewa: “Na san aikina a matsayina na shugaban Najeriya. Kundin tsarin mulkin Najeriya ya fayyace ayyukan gwamnan jihar Kano, don haka da zarar aka ce batu yana gaban majalisar dokokin jiha (kamar yadda yake a kan Kano) shugaban kasa ba shi da damar tsoma baki.”
Ya kara da cewa: “Na sha rantsuwar yin byayya ga kundin tsarin, kuma ba zan sauya matsayina ba.”
Da ma dai tawagar jihar Kano, kamar yadda Gwamna Ganduje ya shaida wa shugaban kasar, ta kkai masa ziyara ne domin ‘nuna godiya’ saboda irin yadda yake mara wa jihar Kano baya ta hanyar samar da abubuwan more rayuwa da tsaro.

Hakkin mallakar hoto
Twitter/@BashirAhmaad
Image caption

Sarkin Bichi, Aminu Ado Bayero (Hagu) na cikin tawagar da ta ziyarci Shugaba Buhari

Karin labarai da za ku so karantawa:

  • Shin Sarki Sanusi zai karbi nadin da Ganduje ya yi masa?
  • Me ya sa gwamnatin Ganduje ke takun-saka da mawakan Kannywood?

More News

Najeriya za ta dena shigo da man fetur a cikin watan Yuni – Dangote

Aliko Dangote mutumin da ya fi kowa arziki a Nahiyar Afirka ya ce Najeriya za ta daina shigo da man fetur a cikin watan...

An ceto mutane 9 daga wani ginin bene da ya ruguzo a jihar Niger

Mutane 9 aka samu nasarar cetowa daga wani ginin bene mai hawa É—aya da ya ruguzo a yankin Sabon Gwari dake garin Minna babban...

An yi faÉ—a tsakanin masu sayar da waya da sojoji a kasuwar Abuja

Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, ta tura jami’an leken asiri zuwa kasuwar Banex – wata kasuwar kayan lantarki da na’urorin sadarwa da ke...

Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Wutar Da Wani Matashi Ya Cinnawa Wani Masallaci A Kano Sun  Karu Zuwa 16

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon wutar da wani ya cinnawa wani masallaci a ƙauyen Gadan a...