Abduljabbar Kabara: Abin da ya sa rundunar ƴan sandan Kano ta gayyace shi

Kiyawa

Asalin hoton, Kano Police Command

Bayanan hoto,
DSP Kiyawa ya ce har yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike

Rundunar ƴan sanda jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta gayyaci Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya bayyana a gabanta a ranar Litinin 12 ga watan Yuli don amsa wasu tambayoyi kan ƙararsa da wani malamin ya kai.

Hakan na zuwa ne kwana biyu bayan kammala muƙabala tsakanin Sheikh Abduljabbar da wasu Malaman Kano.

Sai dai kakakin ƴan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce gayyatar da suka yi wa Malam Abduljabbar Nasir Kabara ba ta da alaƙa da muƙabalar da aka yi da shi ko kalaman da malamin jihar ke zargin sa da yi.

“Wannan gayyata ba ta da alaƙa da wannan zama da aka yi, dama tun kafin a yi wannan zama akwai waɗanda suka shigar da ƙorafe-ƙorafe a kansa, kuma an fara bincikawa, in ji Kiyawa.

DSP Kiyawa ya ce har yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike.

“Dama an sa ranar dawowa don ci gaba da binciken, to kuma yau ce ranar kamar yadda aka sa a baya,” ya ƙara da cewa.

Wa ya kai ƙarar Malam Abduljabbar?

Shugaban ƙungiyar Izala na Kano Sheikh Saleh Pakistan ne ya kai koke wajen ƴan sanda kan zargin cewa Malam Abduljabbar na barazana ga rayuwarsa.

Ya shigar da koken ne a watan Fabrairu, kuma tun daga wancan lokaci Malam Abduljabbar kan je wajen ƴan sanda lokaci zuwa lokaci.

Gayyatar ta wannan karo ta zo ne tun ranar a Juma’a jajiberin muƙalabala, amma Malam Kabara ya nemi uzuri cewa ga abin da ke gabansa yana kuma aikin haɗa littattafai, amma ya yi alƙawarin zai kai kansa a ranar Litinin.

Wasu labaran da za ku so ka kalla

Asalin hoton, Prof Saleh Pakistan Facebook

Bayanan hoto,
Sheikh ya shigar da koken ne a watan Fabrairu kan zarhin Malam Abduljabbar da yi wa rayuwarsa barazana

Ana iya cewa a yanzu Sheikh Abduljabbar yana jiran ganin yadda al’amura biyu za su kaya masa, ɗaya matakin da gwamnati za ta ɗauka sakamakon muhawarar, sai kuma yadda za ta kaya tsakanin sa da Sheikh Pakistan.

Masu sharhi na ganin daga cikin fatan Malam Abduljabbar shi ne gwamnati ta buɗe masa masallacinsa da kuma ba shi damar ci gaba da karantarwa, musamman ganin cewa ya nemi afuwa kan zarge-zargen da ake yi masa.

More News

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...

Yadda rikici a kan gishirin N20 ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a Kano

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun kanen matarsa, wani Magaji Salisu saboda gishirin N20. Dan marigayin,...