Abba Kyari ya kama masu garkuwa da mutane 81 da ke addabar titin Abuja-Kaduna – AREWA News

Hazikin ‘Dan sanda DCP Abba Kyari Sarkin Yaki, dodon masu garkuwa da mutane, babban kwamandan rundinar ‘yan sanda kwararru na IGP-IRT ya samu nasaran farautar wasu gungun masu garkuwa da mutane da suka addabi hanyar Kaduna zuwa Abuja, da kuma masu aikata miyagun laifuka a cikin garin Abuja da kewaye, da kuma wasu daga jihar Taraba

A cikin wadanda aka kama akwai manyan yaran Shu’aibu Dan Kaduna, kuma sune suka addabi hanyan Kaduna da Abuja, amma shi Shu’aibu ya rasa ransa a wani artabu tsakaninsa da ‘yan sanda kwanaki kadan da suka gabata.

Wasu daga cikin wadannan da aka kama kuma sune suka kashe Jami’an ‘yan sanda Inspector Patrick Yuhana da wasu ‘yan sanda a watan August da ya gabata, tsakanin hanyar Abuja da Kaduna, sai kuma ‘yan dafara ta yanar gizo guda goma (10), wato “Internet fraudsters, harda ‘dan kasar Ghana a cikinsu.

Ansami bindigogi kirar AK47 guda takwas (8) da harsashi guda dari uku da arba’in da bakwai (347), da wasu manyan makamai guda 15, Computer guda goma (10), da zunzurutun kudi naira million goma (N10,000,000) wanda suke karba kudin fansa a hannun wadanda suke kamawa.

‘Yan ta’adda kun shiga uku wallahi!, duk ‘dan da yace uwarsa ba zatayi bacci ba, to shima ba zaiyi bacci ba, babu gurbin buya ga masu aikata miyagun laifuka a Nigeria da iznin Allah Jinjina ga DSP Maibindiga, ASP Abdurrahman Muhammad Ejily da sauran dakarun IRT

Muna rokon Allah Ya tsare mana DCP Abba Kyari tare da jama’arsa, Allah Ka kara musu nasaran da tafi wannan. Amin.

More News

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miƙata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaƙi da yiwa tattalin arzikin ƙasa ne ya hana shi bayyana...