Malan Ibrahim Shekarau ya ce akwai rashin fahimta kan batun kudin na mazabu
A Najeriya, Sanata Ibrahim Shekarau ya bukaci da a kara yawan kudin mazabu da ake bai wa ‘yan majalissun dokokin kasar.
Sanata Ibrahim Shekarau ya bukaci da a karawa ‘yan majalisa kudaden aikin mazabu.
A cewar Sanatan da ke wakiltar Kano ta tsakiya kudaden da ake ba su don aiwatar da ayyukan raya yankunan da suke wakilta ba taka kara ya karya ba, saboda haka ba ne ba a ganin tasirin ayyukan.
Malan Ibrahim ya ce akwai rashin fahimta kan batun kudin na mazabu.
A cewarsa wasu ‘yan Najeriya na da tunanin cewa kudin yana zuwa aljihun ‘yan majalisar ne, ba tare da fahimtar cewa aikinsu shine bin sawun kudin don tabbatar da cewa an aiwatar da ayyukan da aka tsar yi da shi.
Ya ce akwai bukatar gwamnatin tarayya ta samar da wata hanya da za a yi rika bibiyar ayyukan da aka shata yi don ganin anyisu ko akasin haka.
Haka ma ya musanta kallon da ake yiwa wannan zubin na ‘yan majalisa a matsayin ‘yan amshin shata, inda ake zarginsu da amincewa da bukatun bangaren zartarwa ba tare da bin diddigi ba musamman kan abinda ya shafi kasafin kudi ba.
Sanata Shekarau ya bayyana cewa fahimtar juna ne yasa ba a samun matsala tsakaninsu da bangaren zartarwa, ba kamar majalisar da ta wuce ba inda aka rika samun rikici tsakanin bangaroran biyu.