Majalisar Dinkin Duniya(MDD) ta bayyana matukar damuwar ta kan rahotannin dake nuna yadda ake sake samun kashe-kashe daga hare-haren da yan kungiyar Boko Haram suke kai wa a jihar Borno.
A wata sanarwa da jami’in tsare-tsare na Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya ya fitar, Edward Kallon ya ce hare-haren idan ba a kawo karshen su ba za su kawo koma baya kan nasarar da aka samu wajen kare rayukan mutane a yankin arewa maso gabas.
Saboda haka ya shawarci gwamnatin tarayya da kuma jami’an tsaro dake yankin da su kara kokarin da suke na kare fararen hula.
Har ila yau wakilin na Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya ya bayyana damuwarsa kan rikicin kabilanci da ya faru a garin Kasuwar Magani dake kudancin Kaduna da ya haifar da asarar rayukan mutane da dama.