Matasa Sun Kone Wanda Ake Zargi Da Kwacen Waya Ƙurmus A Kano

Wani da ake zargi da kwacen waya ya samu munanan raunuka bayan wasu matasa sun kai masa hari a unguwar Dorayi da ke Jihar Kano.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne bayan an zarge shi da yunkurin kwace wayar wata mata, lamarin da ya janyo rikici a wajen.

Shaidu sun ce matar ta samu raunuka yayin faruwar lamarin, inda aka garzaya da ita zuwa asibiti domin samun kulawar likitoci.

Mazauna yankin sun bayyana cewa matasan sun rinjayi wanda ake zargin kafin isowar jami’an tsaro, sannan suka zuba masa fetur suka cinna masa wuta.

Wani direban adaidaita sahu, Abba Tilda, ya ce: “Lokacin da na iso wurin, an riga an dauki matar a abin hawa domin kai ta asibiti.


Daga bisani an dauki wanda ake zargin zuwa hannun hukuma domin gudanar da bincike.

More from this stream

Recomended