
A ranar Litinin ake sa ran shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu zai tafi ƙasar Turkiyya a wata ziyarar aiki da zai kai kasar.
A wata sanarwa da aka fitar ranar Lahadi, mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya ce Tinubu zai kai ziyarar ne domin sake karfafa alakar dake akwai tsakanin ƙasashen biyu da kuma sake lalubo wasu fannoni na haɗin kai a bangaren sufurin jiragen sama, tsaro, cigaban al’umma da kuma kirkire-kirkire.
Onanuga ya ce fannin kuɗi, sadarwa, kasuwanci da kuma zuba jari su ne za su kasance a gaba-gaba akan batutuwan da za a tattauna a tsakanin ƙasashen biyu.
Ya kara da cewa Najeriya da Turkiyya za su rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna kan ɓangaren binciken kimiyya, fasahar makamashi da kauna fannin tsaro.

