
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya share gwamnan Lagos Babajide Sanwo-Olu a ranar Asabar a wurin bikin kaddamar da aikin titin Lagos zuwa Calabar a jihar.
Kaddamar da mason farko na aikin da aka kammala mai nisan kilomita 30 ya samu halartar manyan baki ciki har da tsohon shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, Babagana Umara Zulum gwamnan jihar Borno, Douye Diri na jihar Bayelsa da Bassey Etu na jihar Cross River.
Tinubu ya na gaisawa da bakin da suke a layi a lokacin da yake binsu daya bayan daya suka tsaye.
Amma kuma da Tinubu ya zo kan gwamnan na Lagos sai ya share shi ya mika hannunsa kai tsaye ga gwamnan jihar Kogi Usman Ododo wanda shi ne ke gaban gwamnan Lagos akan layin.
An dauki tsawon lokaci ana rade-radin cewa Tinubu da gwamnan basa shiri tun bayan da aka cire shugaban majalisar dokokin jihar Lagos, Mudashiru Obasa.
Yan majalisar dokokin jihar ne masu yawa suka tsige Obasa daga kan kujerarsa bayan da aka zarge shi da almubazzaranci da kudade amma kuma aka dawo da shi bayan kwana 49 sakamakon sanya baki da shugaban kasar ya yi